Matar Dr. Saiyadee Pg.25~26
Mhiss~B~hal
25
Matar DR. Saiyadee
(Love&Pain Story Based On Reality)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
[P~M ~L]
Dedicated
2 My fantastic sweetheart FATIMA USMAN DIKKO, nagode dah kaunar dah kike
nunamin ina Alfahari dake deary, ANATARE
INSHA ALLAH
Zufa Affan yakeyi kawai yarasa abinda keh masa dad’i she can’t be OK
d’azunan earpiece d’inta ya lalace ahannun shi balle yace earpiece takeji,
lek’awa yake tah gefen gate amman sam babu abinda yake gani, mukullin hannun
shi yakallah kana yaduba ramin keyhole d’in jikin gate yaga pattern iri d’aya
neh without hesitating yayi plugging key d’in ya murd’a cikin sa’a k’ofa
yabud’e ciki yanufa direct bai ganta a pain parlour bah, d’ayan parlour yaduba
yaganta daidai corridor d’in d’akin tah dah alamun rarrafawa tayi daga d’aki zuwa
wajan, ak’asa akwance take kamar babu rai ajikin tah jini koh ina tsoro neh
sosai yakama shi ganin yanda jini yayi yauwa ak’asa kasa ta’ba tah yayi sabida
yanda yaga skirt d’inta ya’baci dah jini cikin hawaye dah tashin hankali yafita
tsakar gida inda yatarar dah bak’in azaune, cikin hanzari yake masu
bayani bah tareda wani ‘bata lokaci bah sukayi ciki dasauri, nan suka sameta
kwance yanda yamusu bayani, d’aga tah sukayi inda d’ayar takuma fita aguje dan
kiran wata Midwifery dake unguwa, cikin mintuna ashirin Midwifery d’in tah
k’araso dah kayan aikin tah Affan babu abinda yake sai kuka yakasa kiran kowa
ma shi yama manta Dr.Saiyadee gabad’aya hankalin shi yayi dubu atashi sai
up~down yake tayi, excusing d’insu Midwife Nafeesah tace yayi, haka badan yaso
bah yafita zuwa main parlour, aikin tah tashiga yi, allurai tah matah sannan
tabata kulawar gaggawa bayan tagama Ummulkhair tah farfad’o, tuni bleeding d’in
yakoma normal saidai ita dai kawai numfashi take, dah taimakon bak’in tasamu
tah k’imsa wa Ummulkhair jiki tareda yi matah wanka, pad dake side drawer tah
dauka tareda pant data gani a bathroom tuni tah shirya tah tsaf cikin wani d’an
k’arramin kayan bacci wanda dah k’adan ya k’arasa gwaiwar tah dan tasamu tasha
iska, har alokacin Ummulkhair numfashi take kawai amman kwata2 batada k’arfi
she’s very weak bisa gado aka d’aura tah sannan aka saka matah drip d’aya
babban Leda, bayan 30mins har tafara motsi dah magana ahankali take fad’in, Ina
Abusaiyeed? Abusaiyeed yakira? Ni ku kiramin Abusaiyeed, shhh midwife Nafeesah
tace matah sannan tashiga matah bayanin abinda yasame tah kamar haka,
Toh
nafarko dai Malama from what I saw u’re ON, kuma MENORRHAGIA is one of the most
common types of abnormal bleeding from the uterus, toh in some cases kuma the
cause of heavy menstrual bleeding is unknown, in some cases kuma some of the
common causes are:
Hormone
Imbalance sabida idan ansamu matsalar hormone Imbalance the endometrium
develops in excess and eventually sheds by way of heavy menstrual bleeding, and
malama kinada Fibroids neh midwife tah tambaya, kai kad’ai Ummulkhair tah iya
girgiza wa alamun A’a, toh kidai je kiduba sabida it can happen very fast kinga
Fibroid shima yanah kawo much bleeding kinsan shi haihuwa yake dazaran kuma
yaje uterus d’inki it can cause heavier than normal or prolonged menstrual
bleeding, sai kuma medication U’re have to be careful when using drugs
especially during menstrual period sabida certain drugs including
anti~inflammatory medications and anticoagulants can contribute to heavy or prolonged
menstrual bleeding, sannan other medical conditions includes pelvic
inflammatory disease (PID), thyroid problems, endometriosis, and liver or
kidney disease is likely to be associated with menorrhagia, wannan kenan we
have so many others, gaskiya mata we need to be extra careful sako nake isarwa
gareku sisters, In severe cases, heavy mensuration can interfere with sleep and
daily activities, LADIES blood loss from heavy periods can lead to ANEIMIA, and
symptoms are fatigue and shortness of breath. Dan Allah mata mukula sosai kada
kiyi amfani dah drugs bah tareda kinyi consulting doctor bah that’s very bad U
know, kiyi avoiding kayan zak’i in excess kuma make sure ur bleeding is normal!
Tnx muhad’u @pg 26
Mhiss~B~hal
26
Matar DR. Saiyadee
(Love&Pain Story Based On Reality)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
[P~M ~L]
Dedicated
2 Mhiss B~hal Yes Myself I love Myself like sosai d’innan
Bayan Ummulkhair tagama jin bayanin Midwife Nafeesah, godiya tayi matah
har yanzu muryan natah bawani fita yakeba mijin ki fah? Wajan aiki kawai tah
iya cewa toh shikenan u’re stable Allah ya sauwake zandawo by 09:30pm tunda
banida nisa sosai nazo naduba ki, godiya Ummulkhair tayi matah hawaye nah zubar
matah tanah tunanin da’ace mijin tah yananan dashi zai matah komai, bak’in tah
neh suka dinga matah sannu duk atunanin su zafin ciwo neh, gida suka tsaftace
matah tas suka yimata sallama sabida duk dah auren su zani tasamu tad’an rufe
jikin tah sannan Affan yashigo, kwance yasame tah kamar yayi kuka duk jikin shi
amace waje yasamu yazauna kan kujera sannan yace, “sannu sis ya jikin naki?
Alhamdulillah, Affan zo katafi gida dare yayi kaga Mummyn mu hankalin tah zai
tashi kuma Dan Allah kada Kafad’a masu komai, Sis bangane kada nafad’a masu bah
dah ban manta dah keys d’inah bah fah? wazai san halin dakike ciki kokuma daba
mukullin gate d’inki nah mu sanya danawa bah daya kenan, haba sis wlh bakisan
yanda hankali nah yatashi bah idan mutum yayi loosing alot of blood mutuwa neh
fah saidai kawai Allah ya tsare, naji lilbro we would talk this ova next time pls
zo kah tafi, it’s late already, yeah zantafi nah yarda amman saikin kira mijin
ki sabida gaskia barin ki keh kadai anan gida dah matsala tunda har yanzu mere
looking at U ma nasan U’re still sick and weak so ki kira yayanmu idan yazo
saina tafi kawai, kaje I promise U yakusan zuwa ai midwife takira shi yananan
tafe, dakyar Ummulkhair tasamu Affan ya yarda yaje gida kuma tasa yayi mata
alk’awarin bazai fad’awa iyayen su bah, baya tafiyar sah takaici neh yarufe tah
asanadiyar rashin wadataccen lokacin dah bata samu daga mijin tah gashi har
bak’i neh en unguwa yau suka shiga matrimonial room d’inta harda wanka akayi
matah kuma wai mijin tah doctor neh babbah wannan wace irin rayuwa ce mesah
Abusaiyeed bazai tsaya ya saurare tabah sabida aikin sah, ita batada gatan
lokacin sah saidai jama’a, kuka tafashe dashi sosai anan baccin wahala yayi
awon gaba dah itah, sai chan wajajan 10 tafarka jin ana buga k’ofa yanzu tad’an
ji dama2 saikuma zazzabi dake k’ok’arin rufe tah tasan bakowa baneh a doorstep
illa Midwife saidai batajin zatah iya tashi, ahankali taduba wayan tah
taga har izuwa lokacin babu kiran Saiyadee cikin bak’in ciki tah tura masa msg
kamar haka,
Eh
tabbas aikin kah yanada muhimmancin gaske wanda koh ni banida shi, kazo ka
dauki gawata kah binne! Abusaiyeed ina makah fatan Alkhairi! haba Khairiya er
arzik’i, bayan tah tura tah kwanta tanajin zuciyar tah kamar zatah buga har
yanzu tanaji ana buga k’ofa har aka daina bata iya tashi bah wani baccin neh
yakuma d’auke tah, ya Saiyadee yanacan yanata faman aiki yaji shigowar msg
amman koh kad’an bai damu yaduba bah sai chan bayan ya amsa wani important call
yaga hanging message daga Ummulkhair hakan yasa yabud’e ya karanta, gumi neh
yafara keto masa time yaduba yaga 11 har tayi babu abinda yasake yi yad’auko
carkeys nashi yayi waje shidai kawai driving yake yanah farautar gidan sah
besan abinda yake bah Allah neh kadai yakai shi gida awaje yayi parking yabud’e
gidan yashige direct yayi d’akin tah, ahankali yabud’e k’ofa yahango tah abin
tausayi kwance akan gado k’arasawa yayi yad’an ta’ba goshin tah yaji zafi
kallon tah yake dah drip dake gefenta kunya yaji sanin sarai wani doctor d’in
aka samo yayi treating d’inta, ranshi neh yayi bak’i yana tunanin Allah yasah
bah namiji baneh yata’ba masah hannun matah wajan saka drip, towel yasamu
yasamu d’an k’arrami yasa aruwa yanah saka mata agoshi in other to relief her
from slight fever’n daya kamata, cikin bacci taji hakan k’amshin turaren sah
neh yasah tasan shine bakowa bah, k’in bud’e idon tah tayi kallon tah yake,
k’arshe tagaji tabud’e ido amman tah kauda kai,
“Wifey”,
yace muryan sa chan k’asan mak’oshi, m so sorry, d’an Allah ki kula ni karna
mutu, Ummulkhair babu abinda tace sai wasu hot tears dasuka fara forming a
idonta rapidly!
Mhiss B~hal Ce

Comments
Post a Comment