Matar Dr. Saiyadee Pg.1~2


[24/07 22:11] 
NoVel WriTter 
Mhiss~B~hal‍
1
‍‍      
     
Matar DR. Saiyadee

(Love&Pain Story Based On Reality)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
               [P~M ~L]
http://www.mhissbhal.blogspot.com
   Alhamdulillah Alhamdulillah cikin Ikon Ya Rabbi Nakuma dawowa acikin sabon littafina mai suna MATAR DR. SAIYADEE INA fatan zaifi ASALIN RAYUWA DAD’I dah darasi,  dafatan kowa yayi sallah lafiya Allah yamaimaita manah Ni Mhiss B~hal Ina muku barka dah shan ruwa All ova pls kada amanta adaura dah Azumin Sitta Shawwal Fans, Allahu ya amshi ibadun Mu baki d’aya, AMEEN
Dedicated to SadNaf dearyLuv U
    
       Kwance take kan gado tayi ruf dah ciki idanta biyu Amman tah rufe su tamkar mai bacci, daga ganintah kasan tanah cikin damuwa dah alamun tayi kuka tayi nak, Oh ni Ummulkhair Allah kazaba min mafi alkhairi arayuwa abinda naji tah fad’i kenan, sallah taji ana kira tamik’e taje tayi alwala tayi sallah bayan tah idar neh tah mik’a hannu kan gado tah dauki wayantah dubawa tayi taga Sam babu missed call dinshi koh daya, jiki asanyaye tashiga dailing numban sa, saida takira sau hudu har tah fidda rai sannan yadauka, 
Salam’alaikum, 
Wa alaiki salam Ummunah, ya kike?
Lafiya kalau Alhdulillahi ya aiki, 
Aiki dah godiya Ummunah gashinan munata fama ai,
Sannu Allah yataimaka kace za…….
Inazuwa inazuwa Ummunah zankira ki aiki nakeyi,
Baiko bari tak’arasa magana bah sai Jitayi phone d’in yayi cutting gabad’aya jikinta yayi sanyi kwanciya tayi kan daddumar tanah kala~kalan tunani har bacci yayi awon gaba dah itah,
  Wacece Ummulkhair?
Ummulkhair d’iya Ce ga Alhaji Abu Sufyan dah Hajiya Hadiza, Su biyu neh kadai awajan Iyayen su daga itah sai K’anin tah Affan, Ummulkhair doguwa Ce height d’intah is average chocolate in complexion very cute tanada k’iba daidai misali, gashin tah shima curly kuma tsayin shi daidai misali atakaice dai Ummulkhair yarinya Ce mai kyaun gaske san kowa k’in wanda yarasa tasamu wadatattan tarbiya daga Iyayen tah Masha Allah, at the age of 15 tagama secondary school d’intah, Cikin Ikon Allah taci Waec&Jamb d’intah tasamu admission at Bayero University Kano inda tah karanci Biological science, at the age of 19 tagama sch d’intah tareda saukan Al~Qur’ani mai girma, Alhamdulillah tayi service at 20yrs, tah kammala komai Lucky her! Ummulkhair tanada wani Saurayi maisuna Abubakar wanda ake kira dah Saiyadee shine Wanda takesan aure in the sense that akwai soyayya mai k’arfi atsakanin su saida kuma kash tanah fargaba sabida amatsayin tah nah ‘yaamace tanah lacking lots of things daga gareshi kasancewar likita neh, she lacks his time&attention amman kuma ahakan suke soyyayar su kullum yanah batah hak’uri akan cewa watarana sai labari dah haka soyayyar su tah d’aure,
Wanene Saiyadee?
   AbubakarSaiyadee d’aaneh ga Alhaji kabeer Fahad dah Hajiya Humaira, shine d’ansu nafari saikuma k’annen sah uku wato Bilal, Amrah dah Autah Amal, Saiyadee yayi karatun sah nah likitanci a ABU Zaria sannan yadawo garin kano yayi bautan k’asa Idan cikin ikon Allah yasamu Offer nah aiki a Private clinic nah International Clinics & Maternity kano, yana cikin wannan neh Allah yakuma d’aukaka sah inda yakuma samun aiki a AKTH Kano, so sai yahad’a biyun hakan bah k’arramin tightening schedules d’insa yayi bah, Saiyadee yakasance mutum mai nutsuwa Wanda koh magana batah damesa bah, kyakkyawa neh, dogo chocolate in complexion, his Smile kills, nutsuwar Saiyadee bah k’arramin Jan hankalin en matah yake bah, hakan yasah suke yauwan damunsa dah zancen so Masha Allah bah maikula matah baneh so one way or the other he’s always avoiding ladies, acikin rashin kula matan nasah Allah yahad’a shi dah watah baiwar Allah a asibiti mai suna Ummulkhair har yakasance shine mai checking d’inta when it comes to health har takaida yazama Family doctor d’insu yasamu karbuwa awajan iyayen tah sosai sabida halayyar sah tagari, Ummulkhair dah Saiyadee sun shak’u sosai tun suna abin nasu kamar brother and sister, har suka fuskanci suna san junansu, tareda alk’awarin aure, saidai kuma atimes suna samin matsala sabida Saiyadee is so devoted to his work itah kuma Ummulkhair tanada zafin kishi amman sabida san datake masah takan danne zuciyar tah akan wasu abubuwan dah take lacking daga gareshi, sosai take kuka wani sa’in amman sam batah ta’ba nunawa agidan su bah sabida tasan iyayen natah suna sanshi kuma sun amince dah abinda ke tsakanin su, saidai kawai idan abin yadame tah sosai takan fad’awa k’anin tah yayi matah addua Akan auran tah dah Abusaiyeed d’intah!
Tofah gawani sabon salo koya zaman auren Saiyadee dah Ummulkhair zai kasance? Kubiyoni muji nima nah k’agu fah
       Mhiss B~hal Ce
 NoVelWriTter
Mhiss~B~hal‍
2
‍‍           ‍‍
Matar DR. Saiyadee
       ‍        ‍
                                 
                                 
                               
(Love&Pain Story Based On Reality)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
               [P~M ~L]
Dedicated 2 khadeejah Masscom
   Bayan Ummulkhair tah tashi daga gajeren baccin daya kwashe tah wayan tah neh first thing data fara dubawa aikuwa taga har lokacin babu missed calls d’in Saiyadee koh kad’an, batayi mamaki bah dan sunsaba irin haka dashi hakan yasah tah murgud’a baki tasoma game abinta, kiran Mummyn tah taji tuni tah tashi batare dah k’ara ‘bata lokaci bah dan amsa kiran Mummyn natah, parlour tafara dubawa batah ganta bah hakan yasah tanufi d’akin tah, sallama tayi kamun tace Mummy gani nazo, “toh khairat shigo manah, cikin nutsuwa tah murd’a k’ofan tashige ciki murmushi tasakar wa Mummyn natah, sannan tace Mummy ganinan, kallon tah mahaifiyar tatah tayi cike dah so sannan tace khairat yau bazamu ci abinci baneh koh laifi mukayi neh, naga bakya zancen dinner neh, laa Mummy laifin meh? bakumin komai bah Wallahi kinga game nake awaya nah duk nah sha’afa bara naje nad’aura, “Mummy meza adafa toh, murmushi Mummy tayi sannan tace waida cewa nayi funkaso dah miyar gyad’a koh? naga Abbanku yanaso, tam Mummy bara nakwaba saina had’a miyan, Mummy nah flour koh wheat? Kiyi mixing both er albarka, tam shikenan Mummy nawuce kitchen idan Affan yadawo kice masa ina kitchen, murmushi kawai Mummy tayi,
tuni Ummulkhair tawuce kitchen tah wanke hannun tah sannan tah kwa’ba flour+wheat d’in tabarshi yatashi batare dah wani ‘batah lokaci bah tafara had’a miyan Fans bakuji k’amshi ya gauraye groups bah, ai Ummulkhair badaga nanba when it comes to cooking, phone d’intah dake kan freezer neh yasoma ringing dubawa tayi taga MyHalf, dasauri tayi picking tasaka akunne murmushi tasoma yi saikuma tayi shuru batace komai, 
Ummunah….
Shuru batah amsa bah,
Ummunah koh fushi kike dani neh?
Sai asannan tace, “uhm uhm bah fushi nake bah,
toh kiyi hak’uri aiki neh yayi min yauwa kema kinsan yanayin aikin namu koh,
Uhm nasani Allah yataimaka, yak’ara d’aukaka,
Ameen Ummunah mekike yi?
Girki nakeyi!
Hmmm kice yau su Mummy zasuci jagwalgwalo,
hmmm bawani nan, dad’i dai,
ahh toh mutum da iyakar sah abinda ya iya dafa ruwan zafi inashi ina wani girki,
dariya tah kyalkyale masah harda rufe fuska kamar yanah gabanta, shuru yayi yanah sauraran dariyar tah mai sakashi farin cikin gaske kaunarta yanah ratsa shi tun daga kai har k’afa, Ummunah yace muryan sah k’asa~k’asa,
Na’am Ya Saiyadee, tah amsa cikin murmushi,
I miss U, yace
I miss U more ai tafad’a kamar maisan yin kuka, 
bawani nan injiwa, nafi missing d’inki kina ganin koh aiki nakasa yi sosai sabida banji muryan ki bah,
hhhh toh naji nikam kaga harna gamayin miya fah,
Ai miyan bazata yi dad’i bah tunda bakiji murya nabah kika yishi
Laa injiwa toh?
Injini mijin Ummulkhair
dariya tayi sannan tace “hakadai kace ya saiyadee amman dah dad’i
toh Ummunah mezakiyi yanzu?
Funkaso zan soya shi kadai yarage min,
toh bara nazo nataya ki karki k’onamin hannun,
chab saikace yarinya ai kona k’one ni macece,
toh kajisu su matah, maza suja gefe
dariya tasaki sosai tace Ya Saiyadee nibance bah,
toh naji Ummunah bara nacigaba dah aikinah anjima zan sato hanya nazo naduba ki, kiyi ahankali kada ki k’one kinji pls, 
toh Saiyadeen Ummu, Insha Allah!
Mezan siyo miki?
Bkomai tah amsa, 
Kin tabbatar babu abinda kikeso,
Eh babu deary,
Toh shikenan later deary bye!
Uhm kawai tace kamar tayi kuka sam bataji dad’in yankewar wayan bah saidah tad’au kunsan 30mins azaune kafin tah dauki funkaso wanda daman yatashi tasoma zuba shi cikin mai, tanayi tanah tunanin Saiyadeen tah gaba d’aya jitayi hankalin tah yakasa kwanciya sotake yau taganshi sun dad’e basu had’u bah sabida yanayin aikin sah, 
Wayartah tah d’auko tamishi message kamar haka,
 Salam Abusaiyeed Dan Allah yau kazo I badly want to see U kagafa U promised, pls stick to your promises dear, I miss U tekia! 
Ajiye wayan tayi tacigaba dah abinda takeyi bayan tagama tazuba komai cikin warmers tayi setting table, d’akin Mummy tawuce straight idan tah sheda matah cewar tah kammala komai hartayi musu ginger drink, sosai Mummy taji dad’i tah dinga matah Addu’oi dah shimata albarka, dariya tayi kana tace bakomai Mummynah hakk’inah neh nah taimaka miki ai, Mummy Dan Allah Ya Saiyadee yace zaizo nan bada jimawa bah, 
toh shikenan maraba d’an Albarka maza kije ki k’imsa kafin yazo, Allahu ya Albarkaci rayuwar Ku baki d’aya!
Ameen tace tah mik’e cike dah farin ciki hartakai bakin k’ofar d’akin tah watah zuciyar tace matah, hmmm sai wani murna kike kamar kin tabbatar dazuwan nashi saikinzo kinyi kwalliyar ki abanza ma baizoba kodai bah Saiyadee bah kinmanta aikin shi yafiye masa komai arayuwa, take taji mood d’inta yacanza tayi deciding taje tad’au phone d’intah tacigaba dah game d’intah kawai bayan tayi wanka,
 On reaching to her phone taga hanging message from MyHalf, murna cikin Ummulkhair ba amagana tuni tah manta dah dukkanin damuwan tah tanah bud’ewa taga reply kamar haka
 “Insha Allah Ummunah dah anyi magrib kafin Isha’i zaki ganni nima I also miss U, sonake naganki heartbeat!
  Tsalle tayi dan murna tuni tayi hanyar fita adaidai k’ofa tah tarar dah Affan tsaye yanah kallon tah yanah dariya kamun yace, “Sis kawo muraba kyautar kud’in dakika samu dake sakaki murna haka!
     Mhiss B~hal Ce


Comments

Popular posts from this blog

Matar Dr. Saiyadee Pg.27~28

Matar Dr. Saiyadee Pg.25~26

Matar Dr. Saiyadee Pg.19~20